Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya amince da nadin sabbin hakimai biyu a masarautar Yauri.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hakiman da aka nada sun hada Muhammed Bello Na’Allah a matsayin Hakimin Makurdi a karamar hukumar Ngaski da Lawal Jibrin Yahaya a matsayin Hakimin Kwanji a karamar hukumar Shanga ta jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Yace Har Ya Yi Hasashen Mutuwar APC Bayan Zaben 2023
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Muhammed Sani Umar, wadda aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
Babban Sakataren ya yi fatan Allah ya yi musu jagora da kariyarsa wajen gudanar da sabbin ayyukansu domin ci gaban yankunansu.
A wani labarin kuma, Gwamnatin na kashe N8.3trn akan jami’anta, amma abun baƙin ciki ba za ta iya baiwa ASUU N1trn ba – Ndume
Sanata Ali Ndume ya soki gwamnatin Najeriya kan ware tiriliyan nairori ga jami’an gwamnati.
Ndume yana son kashi 50 cikin 100 na albashin ‘yan majalisar tarayya da ake warewa kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).