Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sikandire Jamb, ta bukaci masu sanya idanu yayin jarrabawar da su Fallasa masu satar amsa yayin jarrabawar.
Kwanturolan Hukumar na shiyya Sofela Bisi ne ya bukaci hakan, a Minna yau Juma’a, yayin da yake karin haske ga manema labarai kan fara gabatar da jarrabawar da daliban Najeriya suka yi.
Ya ce wasu daga cikin masu kula da daliban kan yi Ƙemagadas da daliban da kan saci amsa, wanda hakan kuma idan aka kama hukunci ne mai tsanani ga dalibin da kuma makarantar.
Ya ce suna sane kuma da Jami’an kula da jarrabawar da kan karbi kudi a wajen dalibai da sunan taimakon su, wanda shima wannan babban laifi ne da idan hukumar ta samu bata yafiya akansa.
Daga nan sai ya bukaci shugabannin makarantun Sakandire a jihar Neja, da su kara sanya ido domin dakile matsalar satar amsa yayin jarrabawar ga dalibai.
A karshe ya bukaci masu daukar wadanda zasu kula da jarrabawar da su kasance mutane na gari, domin a cewar sa hakan ne zai bayar da damar tabbatar da gaskiya yayin jarrabawar da Jamb a bana.