By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kashe gobara ta tarayya reshen Yolan jihar Adamawa tace sun ceto mutane takwas tare da ceto dukiyayar data kai Naira biliyan 3.8 a cikin tashin gobara 64 da aka samu a jihar a shekarar 2021.
Mista Philip Odu, Kwamandan shiyyar Yola ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litinin a Yola.
Yace “Daga watan Janairun 2021 zuwa yau, rundunar ta halarci kiraye-kirayen barkewar tashin gobara 64, inda ta gudanar da ayyukan ceto 11, inda aka ceci rayuka takwas yayin da uku suka rasa rayukansu.
“Haka kuma, a cikin lokacin da ake bitar, an ceto kadarorin da suka kai ₦ biliyan 3.87 yayin da aka yi asarar dukiya ta ₦294.60 a sanadiyyar bala’in tashin gobara”. A cewar Odu.
Kwamandan shiyyar ya bayyana rashin hadin kan al’umma a matsayin babban kalubalen daya ke shafar ayyukan kwamandojin, musamman a lokutan ayyukan su.
A cewarsa, a lokuta da dama ana kai wa jami’an mu hari tare da lalata musu kayan aiki da wasu marasa kishi keyi.
“Bayan hare-haren da wasu marasa kishin kasa ke kaiwa jami’an mu a bakin aiki, jami’an tsaron farin kaya na Najeriya sun hada hannu da wasu jami’an tsaro na sojoji domin tallafa mana da kuma ba mu kariya a duk lokacin da za mu kai dauki domin ceto a lokacin barkewar gobara.” Inji Odu.
Har ila yau, ya bayyana dokar aikin kashe gobara ta shekarar 1963,cewa babu wanda ya bi ka’idojin kiyaye kashe gobara da mazauna yankin da rashin kula da gwamnatocin jihohi kan bukatu da jin dadin aikin kashe gobara a matsayin wasu kalubalen da ke kawo cikas ga ayyukanta.
Dangane da alakar aiki da sauran hukumomin ‘yan uwa, ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alakar aiki.
Shugaban hukumar kashe gobara ya gargadi jama’a da su kaurace wa kiraye-kirayen karya, yana mai jaddada cewa daga yanzu rundunar ba za ta yi wasa da duk wanda aka samu yana aikata wannan lamarin ba.