Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta kashe gobarar da ta kone ofisoshi guda biyar a Makarantar Kimiyya da ke Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST), ta Wudil a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Alhaji Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
“Mun samu kira a sashin mu na Wudil daga jami’an tsaro da misalin karfe 12:04 na dare cewa gobara ta tashi a wani bene na makarantar.
“Bayan samun labarin, mun yi gaggawar aika motar kashe gobara zuwa wurin da abun ya faru da misalin karfe 12:07 na daren, domin shawo kan lamarin,” in ji sanarwar.
Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta kone dukkan ofisoshin guda biyar gaba daya, gobarar wacce wutar lantarki ce ta tashi.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito ya bukaci jama’a da su kara yin taka-tsan-tsan da kuma kulawa a lokacin da ake gobara.