Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta ce zargin satar kudi fam 400 (Naira 223,000) da aka yi wa jami’an tsaron jiragen sama a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), Legas karya ne.
Wani fasinja mai suna Mista Olakunle Tayo Fapohunda, ya yi ikirarin cewa jami’an tsaron Jiragen Sama guda biyu ne suka hada baki, kuma suka kwashe fam 400 daga jakarsa a lokacin da suke bi ta na’urar daukar hoto ranar Laraba, a kan jirgin Virgin Atlantic London Heathrow.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, Babban Manaja na Hukumar FAAN, Misis Henrietta Yakubu, ta ce wani nazari da aka yi na faifan bidiyo na rufe a (CCTV) ya nuna cewa babu wani abu da ya faru.
“Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN) za ta sanar da ku cewa mun yi bincike sosai kan zargin amma mun gano cewa ba gaskiya ba ne, domin babu daya daga cikin jami’an biyu da ya taba kayan kamar yadda hoton bidiyon CCTV ya nuna a fili,” FAAN ta bayyana.
Ta ce ba wanda ya taba kayan sai jami’in hukumar NAHCO, wanda ke bayan Fapohunda, kuma jami’in ne kawai ya tura kayan a gaba domin ya samar da fili da jakarta za ta fito daga na’urar ganin har hanji ta XRay.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun iya tabbatar da cewa a duk tsawon tafiyar Mista Olakunle a wurin tantancewar, babu wanda ya cire komai a cikin akwati.
“Yayin da muke jin daɗin wannan batu kuma muna son mu bayyana masa godiyarmu a kan haka, za mu so mu bayyana cewa Hukumar tsaron Jiragen Sama tana da da’a, wadda ta kwato tare da dawo da abubuwa da yawa da fasinjoji suka manta ko suka rasa a tsawon shekaru.
“Duk da cewa muna lura da cewa ba zai yuwu a samu baragurbi a cikin hukumar ba, muna so mu tabbatar muku da cewa Hukumar ba ta lamunci irin wannan rashin da’a, kuma mun gudanar da wannan bincike da matuƙar kulawa da kyautatawa.”
FAAN ta kuma bayyana a shirye ta ke ta samar da hotunan na’urar CCTV ga fasinja.
“A karshe yayin da muke ba da shawarar cewa ya kamata mu yi taka-tsan-tsan wajen yin zarge-zargen da bai dace ba, domin irin wadannan ayyuka na iya lalata rayuwa da sana’ar wadan da abun ya shafa, za mu kara tabbatar wa fasinjojin mu masu daraja cewa filayen jiragen samanmu suna cikin koshin lafiya, da jami’an mu. Sanarwar ta kara da cewa za su cigaba da gudanar da ayyukansu cikin inganci da kwarewa.
Comments 1