By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar tsaro ta yammacin Najeriya da aka fi sani da Amotekun ta dakile yunkurin wani harin fashi da makami da aka kaiwa wasu matafiya a hanyar Ilesa zuwa Akure.
An bayyana cewa matafiyan suna cikin wata motar bas mai dauke da fasinjoji 18 a lokacin da ‘yan ta’addan suka far musu tare da yin kokarin kwace musu kayansu kafin daga bisani mutanen Amotekun suka bayyana tare da dakile harin.
Shugaban kwamandojin Amotekun na Kudu-maso-Yamma kuma kwamandan Amotekun na jihar Ondo, Akogun Adetunji Adeleye, wanda ya bayyana faruwar lamarin, ya ce barayin sun tsere ne bayan sun yi artabu da rundunar Amotekun.
Ya ce, “Mun samu labarin farmakin da ‘yan fashi da makami ke yi wa fasinjojin da ke tafiya daga Legas. Lokacin da muka isa wurin, direban motar J5 ya bar wajen
’Yan fashin sun bar motar bas suka shiga dajin sai da muka fara tsefe daji bayan ceto fasinjojin, Mun bincika har washegari kafin a gano shi (direba) mil biyar daga wurin da aka kai harin na fashi.
“A karshen ranar, mun sami damar kwato kayayyakin da aka sace. A hanyarmu ta dawowa, mun tarar da wasu mutane a cikin wata motar bas mai mutane 18 sannan kuma mun kwato su daga hannun wasu ‘yan fashi da makami. Mun tuntubi mai wannan kaya kuma nan ba da dadewa ba za a mayar masa da kayansa zuwa jihar Kano.
“Wannan wani bangare ne na Mataki na 7 na Operation Cleanup.”
Kwamandan ya kuma bayyana cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da cewa an dakile munanan laifuka a jihar Ondo da sauran jihohin Kudu-maso-Yamma.