By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da yadda a ke kashe Kudin Kasa, ta karrama Gwamnan Jihar Kano Dakta. Abdullahi Umar Ganduje OFR, a mastayin jajirtaccen shugaba a fannin gudanar da gwamnatin sa a bayyane kuma bisa amana da kuma yadda yake alkinta kudaden Jiha wajen gudanar da ayyukan cigaban al’umma.
Hukumar tace ya zama dole a yabawa Gwamnan bisa rawar ganin daya ke takawa wajen gudanar da mulki wanda yake a bude da kuma amfani da kudin gwamnati wajen samar da ababan more rayuwa ga ‘yan jihar sa.
Shugaban hukumar, Barista Victor Muruako shine wanda ya bayyana hakan a lokacin daya jagoranci jiga-jigan Hukumar inda su ka kai wa Gwamnan ziyara a ofishinsa dake fadar gwamnati a yau Litinin.
Gwamna Ganduje ya yi maraba da jami’an Hukumar sannan ya yaba musu bisa shirya taron wayar da kai akan tsantseni da rikon amana wajen sarrafa kudaden gwamnati sannan ya bayyana aniyar sa ta yin aiki tare da su.
A lokacin ziyarar Gwamnan yana tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Hon. Ali Haruna Makoda da kwamishinoni da shugaban riko na Hukumar Karbar Korafe Korafe, Barista Balarabe Mahmud da sauran jami’an gwamnati.