Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ce dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba ba zai buga wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da Faransa za ta yi ba saboda raunin da ya samu a cinyarsa a ranar Litinin.
Dan wasan mai shekaru 28 ya fice daga horo a sansanin Clairefontaine na Faransa bayan ya hi rauni.
Kungiyar Ole Gunnar Solskjaer ta Man United za ta buga wasa a ranar 20 ga Nuwamba da Watford a gasar Premier.
Hukumar FFF ta ce Pogba ya kasance “wanda ya ji rauni a cinyarsa ta dama”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Anambra: Haryanzu Ba’a Fara Kada Kuri’a ba a Wasu Yankuna na Ihiala
A ranar Asabar ne Faransa za ta karbi bakuncin Kazakhstan, inda take saran nasara, domin ta tabbatar da samun gurbi a gasar cin kofin duniya na badi, kafin wasansu na karshe na rukunin D a Finland mako mai zuwa.
Dan wasan tsakiya na Roma Jordan Veretout ne ya maye gurbin Pogba a cikin tawagar na Faransa.
A wani Labari Kuma na daban.
Gwamnatin jihar Legas tace za a yi wa mutane kusan 400 dake fama da nakasa magani kyauta.
Babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, Dr Olusegun Ogboye ne ya bayyana haka a ranar Litinin a lokacin daya ziyarci wurin tantance sabbin mutanen da suka amfana a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas.
Yace aikin tiyatar gyaran an yi niyya ne domin farfado da mutane musamman yaran dake fama da nakasar kafafu dake shafar lafiyar girmansu na yau da kullun.
A cewarsa, atisayen ya samu sama da mutane 400 da zasu ci gajiyar shirin, wadanda za a tantance su na tsawon kwanaki biyu, inda za a gudanar da gwajin lafiyar daya dace.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa yara 80 ne dai zasu ci gajiyar aikin tiyatar gyaran fuska yayin da wasu za a ba su ilimin motsa jiki, abinci mai gina jiki da kiwon lafiya da kuma na’urorin motsa jiki na taimakawa.
Kazalika yace “Tsarin ya kunshi tantancewa inda likitocin fida ke duba marasa lafiya tare da zabar wadanda suka cancanci cin gajiyar aikin tiyatar da sauran wadanda za su iya amfana da na’urorin taimako da sauran nau’ikan gyaran jiki.”
Jami’in kula da shirin, Dokta Tolulope Ajomale ya bayyana cewa sama da majinyata 6,000 ne suka ci gajiyar shirin tun lokacin da aka fara shi.
Ajomale yace shirin ya rikide zuwa wani shiri na wayar da kan jama’a na tiyata da yawa wanda ke binciko aikin tiyata, jiyya da na’urorin motsa jiki masu taimakawa wadanda ke inganta sakamakon lafiya.