Hukumar Kwastam ta kasa reshen jihar Kebbi ta kama Buhunhunan Naman jaki guda 1,390 da kudin su yakai kimanin naira Milliyan 42 a garin Yauri dake jihar
Shugaban hukumar shiyar Kebbi Conturola Joseph Attach ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Kebbi Babban Birnin jihar inda ya ce, an kwace Naman jaki me Saboda Jakuna na daya daga cikin dabbobin da aka Haramta amfani da su a Yankin.
Acewarsa, An tsare Direban Babban Motar da kuma Mallakin kayan, Kuma za’a gurfanar da su a gaban Kotu nan bada Jimawa ba, yayin da naman kuma za’a birne shi.
“Hukumar reshen jihar Kebbi lokacin da take sintiri ta kama wata Babban Mota Mai lamba ARG 323 XA dauke da Naman jaki. Direban da kuma daya daga cikin wadanda suke Motar sun shiga Hannun Kuma hukumar za ta kawo su shelkwatar hukumar tare da kayan laifin”
“Wani binciken zahiri da aka gudanar kan motar ya tabbatar da cewa, Motar na Dauke da Buhunhunan Naman jaki guda 1,390, yayin da bayanan kudin ya nuna cewa darajar su ya Kai Naira Milliyan 42,534,400, Wanda Kuma wadannan kayan laifi ne wadanda suka sabawa dokar jihar sashi na 63 “Ba” cikin baka, na dokar CEMA CAP C.45 LFN 2004″. cewar shi.
Kazalika ya Kara da cewa ” Naman jaki na naira Milliyan 42 an lalatashi a gaban Wakilan rundunar Yan sanda, DSS da kuma na hukumar NESREA “