By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, reshen jihar katsina a ranar Talata, ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu magunguna masu karfi da suka kai Naira miliyan 6.1 tare da lambar rajistar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa ta jabu.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama mutanen ne a jihar Katsina.
Ko’odinetan na strike force’s, Oseni Olorukooba, ne ya bayyana hakan a Katsina a lokacin baje kolin magungunan da aka kama.
A cewar Olorukooba, jami’an rundunar ne suka kama miyagun kwayoyi a kananan hukumomin Malumfashi da Jibia a jihar.
Sannan yace fasa kwaurin magungunan da aka kama sun hada da “katon 52 na maganin karfin kuzari na EJAC foda, hympashy capsule, amipara plus capsule, bobarak capsule manpower, buhunhunan maganin karfin maza, goldfly, gonorrhea capsule da ginseng kofi manpower.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa
Olorukooba ya kuma bayyana cewa, sauran kayayyakin da jami’an suka kama sun hada da buhu 550 na shinkafar kasar waje, katon din Taliya na kasar waje guda 300, da katan fin sabulun kasar waje 790 da aka boye a cikin biscuits da kwalayen Idomi da kuma wani babur wanda kudin sa yakai naira 104,788,000.
Ya yi nuni da cewa fasa-kwaurin na da illa ga tattalin arzikin Najeriya da harkokin kasuwanci.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa jami’an tsaro za su ci gaba da hana fasa-kwauri a Najeriya.