By Abbas Yakubu Yaura
Masu garkuwa da malaman addini guda biyu a Ayetoro hedkwatar karamar hukumar Yewa-Arewa ta jihar Ogun, sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu bayan sun karbi naira miliyan 2.2 a matsayin kudin fansa.
Masu garkuwa da mutanen da suka bukaci a biya su Naira miliyan 15 kudin fansa bayan sun yi garkuwa da malaman a kofar gidansu jim kadan bayan sun isa wurin taron jama’a, inda daga bisani suka amince su karbi Naira miliyan 2.2.
An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun karbi kudin fansa daga iyalansu duk da kokarin da ‘yan sanda suka yi na cafke su .
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane kimanin hudu sun dauki lokaci suna cin abincin da aka shirya kafin su tafi da Hussein AbdulJelil da abokinsa, Ilyas Muhammed Jamiu ranar Asabar da misalin karfe 10:00 na dare.
Da yake tabbatar da sakin su, babban yayan daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Hussein Ibrahim yace ‘yan uwa da abokan arziki sun ba da gudummawar kudin fansa tare da mika ta ga ‘yan kungiyar domin a sako malaman.
Sannan yace “An sake su yau bayan mun ba su Naira miliyan 2.2 a matsayin kudin fansa.
Kazalika yace, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare a lokacin da su (malaman) suke tahowa a cikin motar Toyota Highlander da dan uwansa ya saya kusan watanni biyu da suka wuce.
“Masu garkuwa da mutane biyar ne kuma da suka zo, sun yi kwanton bauna a wani wuri a cikin duhu kuma sun samu nasarar kama su nan take.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi domin jin ta bakinsa, yace ba a yi masa bayani kan sabon lamarin ba, inda ya yi alkawarin zai tuntubi wakilinmu da zarar ya bincika.