Hukumar Kwastam ta Jihar Katsina a ranar Talata ta ce ta samu Naira miliyan 179.2 a matsayin kudaden shiga a cikin watan Nuwamba 2022.
Shugaban yankin, Dalha Wada Chedi, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu na tsawon lokacin da ake bitar, ya ce rundunar ta samu karuwar kashi 47 cikin dari idan aka kwatanta da abin da rundunar ta samar a watan Oktoban 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NCC Ta Nuna Damuwarta Game Da Bidiyon TikTok, Tayi Gargadi Ga Masu Amfani Dashi
Chedi ya kuma bayyana cewa, a tsawon lokacin da rundunar ta kama wasu motoci 12 da aka yi fasakwaurinsu, da sauran hanyoyin jigilar kayayyaki tare da biyan harajin da ya kai Naira miliyan 19,245, 538.
Wasu daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama sun hada da: shinkafar kasar waje, Taliya, macaroni, da kuma couscous.
Sauran sun hada da: Aya, kayan sawa na hannu, PMS, iskar gas, ruwan mai, da sauransu.
Chedi ya kuma bayyana cewa rundunar ta samu nasarar cafke wadanda ake zargi da yin fasa-kwauri a lokacin da ake bincike.
Sai dai ya kara da cewa za’a bayar da belin wadanda ake zargin ne kawai idan an kammala bincike kan lamarin.
Chedi wanda ya yaba wa mutanen da ke karkashin umurninsa kan nasarar da aka samu ya kuma yaba wa sauran jami’an tsaro ‘yan’uwa a jihar kan hadin kan da ke tsakaninsu, inda ya ce sun nuna kwarewa ta musamman wajen gudanar da ayyukansu bisa ga dokokin tarayya da na kasa.
Shugaban Kwastam na Katsina ya tabbatar da cewa, a duk shekara, “Rundunar za ta ci gaba da samar da ingantaccen dabarun tattara bayanan sirri kan tsaro kan iyakokin kasa, da tabbatar da samar da yanayi mai inganci na hada-hadar kasuwanci tare da kara habaka hanyoyin dakile fasa kwauri domin dakile yaduwar cutar fasakwaurin kayayyaki da ke haifar da babbar barazana ga tattalin arziki da tsaron kasar nan.”
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Guinea-Bissau A Ranar Laraba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a gobe Laraba zai tashi zuwa birnin Bissau na kasar Guinea Bissau wanda za a yi masa ado da babbar lambar yabo ta kasar sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da dorewar siyasar kasar da ke yammacin Afirka.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu.
Buhari zai amsa goron gayyatar da shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissolo Embalo ya yi masa na bikin na musamman a fadar shugaban kasa, wanda zai hada da kaddamar da wata hanya mai sunan sa a babban birnin kasar.