Hukumar Kwastam ta mai kula da yankunan Sokoto da Zamfara ta Najeriya ta ce hukumar ta samar da sama da biliyan biyu, da miliyan dari uku da ashirin da tara, da dubu dari bakwai da sittin da biyar da dari tara da shida, da naira saba’in da shidda da Kobo uku a shekarar 2021.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Tahir Balarabe ya sanyawa hannu kuma ya fitar.
Mista Balarabe ya ce wannan shi ne mafi girman kudaden shiga da hukumar ta tara idan aka kwatanta da shekarun baya.
A cewar sanarwar, Kwanturolan yankin Abdulhameed Ma’aji ya yabawa shugabancin da kwanturola Janar na Hukumar Kwastam Hameed Ali ya bayar kan nasarorin da aka samu a aikin.
Ya ce kokarin babban Kwanturola da na hukumar kwastam ta Najeriya ya samar da jajircewa daga jami’an rundunar da ke gudanar da ayyukansu bisa ga wasu dokoki da ka’idojin hukumar.
Mista Ma’aji ya ce wani bangare na nasarorin da rundunar ta samu shi ne na farko da aka rubuta a kan iyakar Illela zuwa kasashen waje a ranar 25 ga Fabrairu, 2021 wanda ya kara habaka noman Albasa a Sokoto tare da ba da gudummawa ga asusun ajiyar kasashen waje kasar.
A cewarsa, hukumar yaki da fasakwauri ta samu jimillar kamun ashirin da biyu na kayayyakin daban-daban da jimillar kudin harajin da aka biya sama da miliyan dari da tamanin da takwas da dari biyar da dubu tamanin da uku da dari uku da sittin da takwas.
Ya kuma nemi goyon bayan ‘yan kasa da su cigaba da bayar da hadin kai ga wannan aikin na su a kan iyakokin kasar nan.
Ya kuma yaba da tallafin kayan aiki da manyan jami’an hukumar kwastam ta Najeriya ke bayarwa, da kuma hadin kan wasu sassan ma’aikata kamar su Hukumar Leken Asiri (CIU), Rundunar ‘Yan Sanda (CPU), Drill Border, Strike Force, da Federal Operations Unit Zone’. B’ (FOU ‘B’), da kuma sauran Hukumomin Tsaro da masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da waɗannan bayanan.
Ya nemi goyon baya da hadin kai daga shugabannin gargajiya da al’ummomin kan iyaka wajen gudanar da ayyukansu yana mai jaddada cewa hukumar kwastam ba za ta iya yin hakan ita kadai ba.