Hukumar Kwastam ta Najeriya, mai kula da Sokoto da Zamfara, ta yi kira ga jama’a da su marawa hukumar baya a kokarinta na yakar ayyukan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Tahir Balarabe ya sanya wa hannu, bayan da wasu fusatattun ’yan daba suka kai wa wasu jami’an hukumar kwastam ta Najeriya hari a sashin Asara da ke Illela kan iyakar Sakkwato da ke karkashin ikon rundunar.
Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar ta Kwastam, Kwanturola Abdulhameed Ma’aji, yana mai cewa, rundunar ta sanya duk wani mataki na dakile fasa kwaurin haramtattun kayayyaki cikin kasar.
Ya ce, daya daga cikin jami’an rundunar ne da kyar ya tsallake rijiya da baya yayin da motar da ke dauke da haramtattun kayayyaki ta yi yunkurin kakkabe ma’aikatan da suka tsallake rijiya da baya kafin motar ta karkata suka yi karo da wata motar da ke zuwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda.
Ya ce sabanin ikirari na cewa an kona motocin kwastam guda biyu, Konturola na yankin ya ce motar rundunar guda daya ta kone, daya kuma na wani jami’in hukumar kwastam hukumar ta Najeriya ne.
Ya ce ya zama wajibi ga ‘yan Najeriya su tallafawa hukumar kwastam don kare iyakokin kasar daga miyagu masu safarar makamai, muggan kwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki don kawo cikas ga kokarin gwamnati na yaki kan matsalar rashin tsaro a kasar.