By Ishaq Dabai
Jami’an hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa, NDLEA tace sun cafke wani dan Najeriya, Okey Eze, wanda ke ikirarin zama dila a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja dauke da hodar iblis guda 350 wanda kudin ta ya haura sama da naira biliyan 2.3.
Sanarwar da Femi Babafemi, Darakta, Kafafen Yada Labarai da bayar da shawarwari ya ce “Eze mai shekaru 38, daga Kogin Orji, a karamar Hukumar Oji River ta Jihar Enugu an kama shi a ranar Laraba 22 gawatan Satumba 202,a jirgi mai lamba 911 yana kan hanyar zuwa Bamako da Addis Ababa da kuma zuwa Abuja.
“An boye haramtaccen kwayoyin mai nauyin kilogram 7.70 a cikin fakitoci takwas da aka jibge a sassa daban daban na kayansa.
“A cikin ikirarin nasa, Eze, mazaunin Bamako, Mali, ya ce ya yi tattaki zuwa Mali ta kan iyakar Seme Badagry ta jihar Legas tun daga shekarar 2019.sannan kuma yace ya shigo Najeriya da kwayoyin ne saboda yana bukatar tara kudi don kula da‘ ya’yan kannensa manya guda hudu.
“Wanda ake zargin ya kuma yi ikirarin cewa ya nemi abokinsa da ke zaune a Brazil daya taimaka masa da wasu kudade amma ya ki, maimakon haka yace masa ya dauki jakar da kwayoyi ta wajen abokina a Addis Ababa dake kasar Habasha kan kudi N500, 000 idan yayi nasarar isar da kayan zuwa ga wanda za a aika masa lambarsa idan ya isa Najeriya.“Ya kuma ce an ba shi jakar dake dauke da kwayoyin a safiyar Laraba a filin jirgin saman Addis Ababa.
Babban shugaban Daraktan Hukumar ta NDLEA, Brig.Janar Mohamed Buba Marwa Mai ritaya, ya yabawa Kwamandan, da jami’ai da mazauna rundunar NAIA bisa taka tsantsan.
Yace sabuwar hukumar ta NDLEA a karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da magance bugun gaba gadi a kan wurare daban daban da ke kokarin mayar da Najeriya cibiya ta muggan kwayoyi.