By Ishaq Dabai
Wani yaro mai suna Umar Ali mai kimanin shekara 15, ya fada cikin ruwa bayan da yaje yin wanka tare da abokansa dake garin Bela ta Dan Madanho a karamar hukumar Ungogo ta jihar kano.
Bayan fadawar sa ne ‘yar uwarsa mai suna Safiya ta kira jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano dan kawo masa agajin gaggawa.
Inda kuma tuni hukumar ta daukoshi daga cikin ruwan dan ceto rayuwar sa sai dai kuma sun sameshi baya cikin hayyacinsa, bayan daukoshi ne aka tabbatar daya mutu.
Jami’in hulda da jama’a na na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar hadarin, inda yace sun mika gawar tasa zuwa ga dan uwansa mai suna Musa Sani danyi masa jana’iza.