A yau litinin ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gurfanar da dakataccen mataimakin kwamishinan yan sandan kasa DCP Abba Kyari bisa zarginsa safarar miyagun kwayoyi.
Wadanda ake tuhumar Kyari dai sun hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba, John Nuhu, yayin da ASP John Umoru kuma aka ce yana can.
Sauran sune Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.
Lokacin da aka karanta wa wadanda ake tuhuma tuhume-tuhume takwas, biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Umeibe da Ezenwanne sun amsa laifin da ake tuhumar su da su, amma Kyari da jami’an sun musanta aikata laifin.
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa tana neman Kyari ne bayan da ta samu faifan bidiyo da ke nuna yadda ya ke tattaunawa da masu bincikenta kan cinikin kwayoyi.
An kama sauran wadanda ake tuhumar ne a ranar 19 ga watan Janairu a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu, inda suka amsa cewa su ne masu jigilar kwayoyi.
Comments 1