Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane 59 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne a Sokoto, ciki har da wanda ake zargi da hannu wajen kashe jami’inta.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Muhammad Iro ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce tun da farko an kama wanda ake zargin wanda ba a bayyana sunan sa ba a watan Janairu a kauyen Bagarawa da ke karamar hukumar Bodinga.
Karanta nanShugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Tsohon Manajan Darakta Na NNPCL Thomas
A cikin haka ne, wanda ake zargin ya sanar da mutanen kauyen da suka taimaka masa ya tserewa kama shi, wanda hakan ya kai ga farmaki kan jami’an mu tare da kashe daya daga cikin su.
Iro ya fusata kan rashin tallafin da al’umma ke ba hukumar, inda ya jaddada bukatar jama’a su san nauyin da ke wuyansu,na taimaka wa jami’an tsaro da sauran jami’an gyaran tarbiyya domin kama duk wasu bata gari a fadin Jahar.
A wani labarin kumaKungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bayar Da Naira Miliyan 180 Ga Al’ummar Tudun Biri
Wani dillalin miyagun kwayoyi yana lalata makomar yaranku, kuma maimakon ku taimaka mana wajen kama shi, kun fito kuna kai mana hari duk da haka, bayan kun sake shi da karfi, ku je ku kashe daya daga cikin jami’anmu wanda hakan ko kusa bai kamata ba in ji kwamandan.
Ya ce wanda ake zargin yana cikin jerin sunayen hukumar NDLEA da na ‘yan sandan Najeriya da ake nema ruwa a jallo a jahar taa Sokoto.
Iro ya bayar da tabbacin cewa wanda ake zargin zai fuskanci cikakken hukumcin doka kuma za a gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a ciki.