Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta fuskanci suka daga Gwamna Abdullahi Sule, wanda ya zargi jam’iyyar adawa da tayar da tarzoma ta addini da kabilanci da gangan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu a zaben.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin jama’a, Mista Peter Ahemba, ya bayyana wadannan matsalolin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a garin Lafia jiya.
Karanta nanHukumar NDLEA Ta Kama Wanda Take Zargi Da Kashe Jami’intaA Sokoto
Ahemba ya yi zargin cewa jam’iyyar PDP ta yi kamfen ne don bata sunan bangaren shari’a tare da kitsa zanga-zanga a babban birnin jihar biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na baya-bayan nan.
A cewar Ahemba, kungiyar Coalition of Indigenous People of Nasarawa State, da ake zargin jam’iyyar PDP ne ta dauki nauyinta, ta kira wasu ‘yan jihar a matsayin ‘yan kasashen waje a lokacin zanga-zangar da aka gudanar.
Ya kara da cewa irin wadannan kalamai na raba jihar bisa kabilanci, ba a taba yin irinsa ba a yankin da kungiyoyi daban-daban suka yi zaman tare cikin lumana.
Ahemba ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta ci gaba da tayar da hargitsi tun bayan yakin neman zabe da ya kai ga zaben gwamna da za a yi a ranar 18 ga watan Maris.
A Wani labarin kumaKungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bayar Da Naira Miliyan 180 Ga Al’ummar Tudun Biri
Duk da gargadin da hukumomin tsaro suka yi na a guji tada rikici, ana zargin jam’iyyar adawa ta ci gaba da kokarin tada zaune tsaye a jihar.
Ahemba ya kuma soki jam’iyyar PDP da yin kira ga kasashen duniya da su tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jihar, inda suka yi la’akari da hakan a matsayin wani yunkuri na ciyar da wata manufa ta kabilanci.
Ya bukaci hukumomin tsaro da su lura da kalaman ‘yan adawa, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da kiyayya a tsakanin ‘yan kasa.