Hukumar kula da yanayi ta kasa, NiMET ta yi hasashen samun ruwansama kamar da bakin kwarya, a wasu yankuna na kasar nan, nan da kwanaki uku masu zuwa,
Babban jami’in Hulda da jama’a na hukumar ta NiMET Mr Ibrahim Muntari ne ya bayyana hakan a cikin wata sanar wa da ya fitar yau juma’a garin Legas.
Muntari ya kuma kara da cewa, hasashen yanayin na kwanaki uku, ya zo ne da ga Ofishin kula da yanayi ta kasa dake hukumar, inda ya kara da y cewa, za’a sami ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi, Adamawa, Taraba, Bauchi da kuma jihar Kaduna.
A cewar shi, sauran jihohin sun hada da: Jigawa, Gombe, Kano da Yobe, Niger, Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma jihar Nasarawa. Inda dunkannin su ake hasashen samun ruwan saman mai karfin gaske.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnan Osun ya ai’yana Litinin a matsayin ranar hutu
Kazalika Mai magana da yawun hukumar ya kuma Kara da cewa, a kwai yuwar samun makamancin irin wannan ruwan sama a wasu yankuna na kasar nan, irin su Benue, Bauchi, Plateau, Kudancin Borno, Gombe, da kuma Kudancin Jihar Yobe.
Muntari ya kuma ce, da yuwuwar samun hazo-hazo, da kuma matsakaicin ruwan sama a sauran sassan kasar nan.
A karshe Muntari ya bayyana cewa, Hukumar ta NiMET na shawartan al’umar dake zaune kusa da rafuka, da su yi gaggawar Kaurace wa yankin, har nan da lokacin da ruwan sama zai ja da baya.
Ya kuma ce, Hukumar za ta cigaba da bibiyar yanayi, da kuma sanar da al’uma da zarar ansami chanji.
Comments 1