By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC, reshen jihar Delta, sun cafke wasu mutane 11 da ake zargin barayin bututun mai ne a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Emeka Peter ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Asaba.
A cikin sanarwar, kwamandan jihar, Abiodun Iskilu, ya ce barayin da ake zargin masu shekaru tsakanin 32 zuwa 66, an kama su ne suna safarar bututun danyen mai da suka lalace a Evurode da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu.
Ya ce jami’an Operation Delta Safe na Sojojin Najeriya sun mika wadanda ake zargin ga hukumar NSCDC saboda hadin kai da hadin gwiwar kungiyoyin biyu.
Ya ce hukumar NSCDC ta kuduri aniyar fitar da duk wasu masu aikata laifuka da ke aiki a jihar.
Iskilu ya yi alƙawarin zafafa yanayin tsaro domin ba za a iya jure wa masu aikata laifuka yin aiki a Delta ba.
Yayin da yake tabbatar wa al’ummar jihar Deltan cewa su ci gaba da gudanar da sana’arsu ta halal ba tare da fargabar tursasawa ko cin zarafi ba, ga masu aikata laifuka a fadin jihar.
kwamandan NSCDC ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala cikakken bincike.
(NAN)