By Abbas Yakubu Yaura
Fitacciyar jarumar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Usman, wacce aka fi sani da Fati Slow ta ce ta gaji da tambayar da ake yi mata yaushe za ta yi aure.
Jarumar wadda tana cikin daya daga cikin fitattun fuskoki a masana’antar, ta shafe tsawon sama da shekaru 15 a masana’antar ta shirya fina-finai.
Kwanan nan ta shiga rikici da babban mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waka, kan zargin yin lalata.
Da take zantawa da sashin Hausa na BBC kan girma da sana’ar fim, ta bayyana yadda tace ta gaji da tambayar da ake yi mata lokacin da za ta yi aure.
“Tambayar da na fi gajiya da ita, kuma mutane sukan yi mini amfani da ita, ita ce lokacin da zan yi aure.”
“Kuma a koyaushe ina tunanin cewa mutuwa da aure duk sun shafi makomar mutum. Na yi imani cewa Allah bai manta da ni ba.
“In Allah ya yarda zan yi aure, zan yi. Kuma idan ya so in koma gare shi banyi aure ba, ba wanda zai iya ya aure ni. Haka Allah yake aiki,” in ji Fati.
Dangane da takaddamar da ta yi da Sarkin Waka, inda ta yi wani faifan bidiyo tana kiransa mazinaci (a matsayin martani ga ikirari da mawakiyar ta yi na cewa wasu ’yan fim ne ke neman wasu ’yan fim mata su yi lalata da su kafin a raba musu mukamai), ta ce ta yi nadamar zargin kuma ta nemi gafara.
“Na fadi wasu maganganu na rashin adalci guda biyu game da shi (Naziru) wanda daga baya ya dame ni har na kasa yin barci a daren,” in ji ta.