By Abbas Yakubu yaura
A ranar Alhamis ne hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC reshen jihar Ogun ta gurfanar da wani mutum mai suna Rojaiye Balogun mai shekaru 65 da laifin yiwa diyar sa mai shekaru 17 fyade, (wanda aka sakaya sunanta) .
Da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar hukumar NSCDC dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Mista Kolawole Taiwo, kwamandan jihar, yace wani na kusa da yarinyar ne ya kai rahoton lamarin ga sashin yaki da fataucin bil-Adama na rundunar ‘yan sandan jihar.
Taiwo yace lamarin ya faru ne a Imomo-Ijebu dake karamar hukumar Ijebu ta Arewa maso Gabas a jihar.
Sannan ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya kwana da diyar sa, inda yace aikin shaidan ne ya sashi yin lalata da diyar cikinsa.
Kazalika ya kara da cewa za a binciki lamarin kuma idan aka samu wanda ake tuhuma da laifi za a gurfanar da shi a gaban kuliya, inda yace iyaye maza wadanda ke cin zarafin ‘ya’yansu mata ya zama ruwan dare a cikin al’umma.
Kwamandan ya bayyana cewa iyaye a bisa dokar kare hakkin yara suna da hakkin kare ’ya’yansu, ya kara da cewa iyaye da masu kula da su su tabbatar suna kula da ‘ya’yansu a kowane lokaci.
Wanda ake zargin ya ce, sau daya ne ya kwanta da wanda aka azabtar a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa unguwa.
Balogun, wanda ya yi nadamar abin daya aikata, yace wanda abun ya shafa din ba diyarsa ce wadda ya haifa ba, inda yace mahaifiyarta ta kawo ta gidan sa tun tana yar shekara 10 a duniya.
Da take magana da dan jarida, wadda iftila’in ya afkawa tace mahaifinta ya kwana da ita da karfi har sau hudu, tana mai cewa karya yake yi cewa shi ba mahaifinta ba ne.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wanda lamarin ya shafa Tace na karshe da ya yi amfani da ita, ya yi mata alkawarin zai ba ta Naira 1,000 domin ya kwana da ita, amma ta ki, a lokacin ne ya kwana da ita da karfi.sannan tace ta kai rahoton lamarin ga mahaifiyarta da yawa amma ba ta yarda da ita ba.