Hukumar NYSC Da CBN Zasu Hada Kai Wajen Amfani Da Tsarin E-NairaHukumar masu yiwa kasa hidima, NYSC, na shirin gabatar da E-Naira ga duk yan kasar nan dake cikin shirin.
Hukumar NYSC za ta hada gwiwa da babban bankin kasa, CBN kan yadda ake amfani da kudin yanar gizo ga mambobin kungiyar.
KU KARANTA: Ku shirya takaddun mika mulki – sakon APC ga gwamnan PDP
Tsarin zai saukaka wajen biyan kuɗi ba tare da haɗari ko fargaba ba.
Mataimakin daraktan yada labarai na bankin CBN, Habib Yusuf ne ya bayyana haka a ranar Litinin din nan, lokacin da ya jagoranci wasu ma’aikatan bankin a ziyarar ban girma da suka kai hedikwatar hukumar NYSC ta kasa da ke Abuja.
A cewarsa, tsarin e-Naira zai ba da damar shigar da masu hidimar kasar da dama domin dai su Amfana.
Ya ce E-Naira kuma za ta baiwa masu amfani da ita damar yin sabbin abubuwa da dama cikin sauki.
Da take mayar da martani ga bukatar babban bankin na CBN na hadin gwiwa, Misis Christy Ifeyinwa Uba, mukaddashiyar shugaban NYSC ta yabawa babban bankin bisa wannan sabon tsarin.
Ta ce NYSC a shirye take kuma a shirye take ta hada kai da CBN ko wata kungiya a kan duk wani sabon salo da zai sanya kyautatuwar yan hidimar kasa.
A wani labarin kuma: Everton Na Son Yin Duk Mai Yiwuwa Domin Mallakar Wayne Rooney
Everton na kokarin shawo kan Wayne Rooney ya maye gurbin Frank Lampard a matsayin kocinta.
An kori Lampard ranar Litinin tare da Toffees a cikin mummunan yanayi, wanda fuskar kowa babu dadi.
Jaridar Goal ta ruwaito cewa kungiyar ta Premier ta tuntubi Rooney a zahiri, domin tana ganin zata iya cika fatan da take da shi akan halin da suke ciki yanzu haka.