Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce sakamakon binciken da ta gudanar a kan Tukur Mamu abin mamaki ne.
Ga dukkan alamu da ta ke mayar da martani kan kalaman malamin addinin musuluncin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce hukumar ba za ta hankalta ba.
Gumi dai ya zargi hukumar DSS da ta’addanci, inda ya kalubalanci hukumar ‘yan sandan farin kaya, da ta gaggauta sakin Mamu wanda shi ne mashawarcinsa kan harkokin yada labarai, ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu nan take.
”Ku kai shi kotu don fuskantar shari’a. Tsare shi a gidan yari duk da kasancewarsa magidanci, an tsare shi ne kawai don tsoratar da shi. Wannan tsoratarwa kuma ta’addanci ce. Kama mutane bisa zalunci, shi ma ta’addanci ne; kamar yadda ‘yan ta’addan ke yi ta hanyar zuwa gidan wani su yi garkuwa da shi,” in ji Gumi.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadin nan, kakakin rundunar ‘yan sandan farin kaya, Peter Afunanya, ya ce a bar hukumar ta DSS ita kadai domin gudanar da aikinta.
Afunanya, ya ce hukumar ta DSS ba za ta yi karin bayani kan kamun da aka yi wa Mamu ba tunda kotu za ta tantance matakin da ta dauka.
“Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bibiyi, tare da lura da yadda wasu sassan jama’a suka yi cece-kuce da al’amuran da suka shafi kama Tukur Mamu da bincike.”
“Yana fatan kada ya shagala da wasu ruɗaɗɗen labarun da suka mamaye sararin watsa labarai.
“Maimakon haka, yana neman a bar ta ita kadai domin ta mai da hankali kan binciken da ake yi, wanda sakamakonsa ya kasance mai ban mamaki.
“A halin da ake ciki, ayyukan hukumar za ta daina yin tsokaci kan batun tun lokacin da Kotun za ta yanke hukunci.
“Saboda haka, an umurci jama’a da su daina furta kalaman da ba a tsara su ba, sannan su jira zaman kotu.”
Mamu ya shiga tsakani yan bindiga da yan uwan wasu fasinjojin jirgin Kasa da aka sace a watan Maris.
A wani labarin kuma: INEC: Jerin Sunayen Da Aka Tantance Ya Sabawa Tsarin Mulkin Kasa, Inji Falana
Babban Lauyan Najeriya Femi Falana ya yi Allah-wadai da zaben mutane 14 da aka tantance a matsayin kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC).
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin nan, Falana ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza yin aiki da tanadin kundin tsarin mulkin kasar wajen tantance mutane 14.