Kasar Saudi Arabia ta Yanke wa Wasu sojin ta uku hukuncin Kisa bisa samun su da laifin zangon kada wa kasar.
Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito cewa sojin syn haɗa kai da wasu da kasar ta kira abokan gaba, ko da yake ba ta fadi takamaiman ta ina wace fuska sojin suka taimaka wa mutane suke wa kasar zagon kasa ba.
Sojin uku da aka yanke wa hukuncin kisar sun hada da Muhammad Bin Ahmad, Shaher bin Issa da kuma Hamoud bin Ibrahim, hukuncin da aka yanke ba tare da bayyana wanene suke wa aikin ba.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta ce ta yi wannan hukunci ne a Rundunar Sojin Kasar dake Kudanci iyaka da Ƙasar Yemen, inda nan ne fakarun sojin Saudiya ke yakar mayakan Houthi na ƙasar Iran.
Wannan Hukunci na zuwa ne daidai lokacin da aka naɗa Yariman Saudiyya Mohammad bin Salman a matsayin Mai Jiran Gadon Sarautar Kasar.
Tsawon Shekaru uku Kenan dai kawo yanzu Yariman yake zartar da tsattsauran hukunci kan iyalan gidan sarautar kasar manyan yan kasuwa da Malaman addini gami da yan rajin kare hakkin Bil’adama