Hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta tursasawa gwamnatin Mali yin bayani kan zargin da ake yi wa jami’an tsaron ta na yi wa wasu mutane kisan gilla a boye da kuma bacewar da wasu mutane da dama suka yi a baya bayan nan.
Human Rights Watch ta ba da misalin mutane 14 da aka yi wa ganin karshe a cikin watan Satumba tsare a hannun jami’an tsaron Mali, kuma tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsu ba.
Bukatar ta kungiyar kare hakkin dan adam din ta zo ne gabannin tattaunawar da ake yi yau Asabar tsakanin wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatin Mali a Bamako babban birnin kasar, don matsawa hukumomin soji sake mikawa farar hula mulki, bayan juyin mulki har sau biyu cikin kasa da shekara guda a kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da hare -haren mayaka masu ikirarin jihadi.
Tawagar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar dake Malin dai ta kunshi manyan jami’an Diflomasiya daga kasashen China, Indiya, Rasha da Amurka, wadanda kuma za su ziyarci Jamhuriyar Nijar a gobe Lahadi.
Bayaga jami’an gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, wakilan majalisar dinkin duniyar 15 za su gana da kungiyoyin farar hula kan karfafa cibiyoyin dimokaradiyya a kasar.