Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka masu alaka, ICPC, ta gurfanar da wani ma’aikacin gwamnatin jihar Yobe, Mohammed Ali Garba, a gaban kuliya bisa laifukan da suka hada da karbar kudi, sojan gona, da kuma yim jabun takardu.
Garba ya gurfana a gaban mai shari’a M.A. Hassan na babban kotun birnin tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis.
A tuhumar mai lamba: CR/478/2022 da aka shigar a gaban kotun sauraron kararraki, ICPC na zargin wanda ake tuhumar ya karya takardar aikin bincike na binciken da ake yi kan Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kogin Oji, wanda ake zargin daraktan ayyuka na Hukumar ne ya sanya wa hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Shafi ‘Yan Najeriya Miliyan 4.4 – Majalisar Dinkin Duniya
Hukumar ta kuma yi zargin cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wasikar bogi na gudanar da bincike wajen karbar kudi har miliyan uku da Naira Dubu Dari Biyar (N3.5m) daga cikin maganar da aka ce zai sasanta da Daraktan Ayyuka wajen “kashe binciken da babu shi.”
A wani bangare na tuhume-tuhumen, ICPC ta zargi wanda ake tuhuma da yin karya ta hanyar bayyana cewa bai ci gaba da karatunsa ba fiye da matakin firamare a lokacin da a zahiri ya yi digirin digirgir a fannin ilimin harsuna/ Turanci daga jami’ar Maiduguri.
Laifukan nasa sun sabawa, kuma ana hukunta shi a karkashin sashe na 364 na dokar Penal Code, da sashe na 10 da 25 na dokokin cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka na shekarar 2000.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa a lokacin da aka karanta masa kunshin tuhume-tuhumen,daga nan sai lauyoyin sa A.D. Atanda da M.K. Akanbi suka gabatar da bukatar neman beli a madadin wanda suke karewa wanda lauyan masu shigar da kara, Mashkur Salisu bai yi adawa da shi ba.
Don haka an dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Janairun 2023 domin tantance neman belin.
A halin da ake ciki, Alkalin ya ba da umarnin belin da Hukumar ta bayar tun da farko ya ci gaba da zama.
A wani labarin kuma, Taron Amurka Da Afirka: Shugaba Buhari Ya Gana Da Biden A Fadar White House
Shugaba Buhari a ranar Laraba 14 ga watan Disamba ya gana da shugaban kasar Amurka Joe Biden a birnin Washington DC.
Hotunan da fadar shugaban kasa ta raba sun nuna shugaban kasar a ganawarsa da Biden da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a fadar White House a gefen taron shugabannin Amurka da Afirka.
Taron na Amurka da Afirka, wanda aka fara a shekarar 2014, shi ne taro mafi girma na kasa da kasa da aka gudanar a Washington tun bayan barkewar annobar COVID-19.