Fitaccen dan siyasa, Buba Galadima ya ce akwai yiwuwar ‘yan bindiga su karbe gwamnatin Nijeriya daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.
Fitaccen dan siyasar ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar DAILY POST, inda ya yi nuni da cewa; sakamakon yadda gwamnatin Tarayya ke kawar da kai ga batun satar mutane har aka koma ana sace dalibai.
Dattijon ya kuma ce tsoffin shugabannin hafsoshin ba su da daidaito kuma hakan ya ba da damar ci gaba. “Gwamnatin Tarayya ta dauki wannan lamarin kamar sanya safar yara. Idan ‘yan bindiga suna da tsari sosai, za su iya karbar mulkin Nijeriya.
“Don haka wannan lamari ne mai muhimmanci wanda ya kamata gwamnati ta ba da cikakken kulawa da kuma kimar da take da ita, wannan abu na iya cinye mu duka.
“Kuna iya ganin cewa tsoffin kwamitocin hafsoshin da suka bar ofis ba su da daidaito, kuma wannan ya ba da damar wannan batun ya bunkasa. Ko a yanzu, idan Shugabannin Ma’aikatan ba su tafi tare ba ba, matsalar ba za ta kau ba”, ya lurantar.