Mawakin Najeriya, Timaya ya ce idan baka da masu gidan rana wato kudade babu wanda zai mutunta ka.
Timaya ya bayyana hakanne a shafin sa na Tweeter da aka tabbatar a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Allah Ne Kadai Ya San Gobe” Dalibai Musulmai a Najeriya Sun Yanke Shawara Kan Wanda Zai Gaji Buhari
Biyo bayan Kalaman nasa dai ya haifar da martani da dama daga sassa daban-daban na duniya.
A wani labarin kuma, Ku Daina Caccakar Obansanjo Saboda Ya ce Peter Obi Ne Zabinsa — Shehu Sani Ga Yan adawa
Tsohon dan majalisar Dattijai Shehu Sani ya bukaci ‘yan siyasa da su daina cacckar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan shawarar da ya yanke na amincewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a zabe mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Idan za a iya tunawa cewa, Obasanjo a sakonsa na sabuwar shekara a ranar Lahadi ya bayyana cewa, ya na goyon bayan tsohon gwamnan Anambra a kan sauran ‘yan takarar da ke neman shugabancin kasar nan.
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC , Bola Tinubu da takwaransa na jam’iyyar PDP, sun nuna bacin ransu kan amincewar da Tsohon shugaban ya yi.
Da yake mayar da martani kan cece-kucen, Shehu Sani ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na da hakki na radin kansa, yana mai jaddada cewa bai kamata ai ta sukar sa ba saboda zabin da ya yi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya rubuta cewa, “Obasanjo ya yi zabinsa. Ya cancanci ra’ayinsa. A dena sukarsa.
“Wadanda bai amincewa da su ba su nemi amincewar Gowon, IBB ko Abdulsalam, su ma tsofaffin shugabannin soja da na siyasa ne masu gaskiya. Haka kuma akwai Ordinary President na Berekete Family Radio”. Inji shi.
A wani labari kuma, Yanzu-Yanzu: Gwamnan Bauchi Na Daf Da Yin Watsi Da Tafiyar Atiku
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi zai yi watsi da bangaren Atiku a hukumance, tare da komawa bangaren gwamnonin G5.
A cikin wasikar da ake “zargi” ya aikewa Shugaban Jam’iyar na kasa Iyorchie Ayu an yi kirarin ya ce, “Da yuwuwar na aje matsayina a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa domin in samu natsuwar samar da wasu matakai da tsare tsaren da ka iya taimakawa dukkanin yan takarar jam’iyar PDP da ni kai na, wajan lashe zaben dake tafe, idan ba a magance matsalar da ake fuskanta ba.”