Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya kare matakin Mikel Arteta na yin watsi da tsohon mukaminsa na mataimakinsa a Etihad domin karbar jagorancin kungiyar Kwallon kafa ta Arsenal. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Guadiola ya ce ko shi ne ba zai dau wani mataki da ya sha banban da wanda Arteta ya dauka ba musamman ma idan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce ta kira shi da ya koma.
KARANTA WANNNA LABARIN: Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Mai 39, Sun Kama Barayin Da Suke Barnar
Dan kasar Sifaniyan ya ce, cikin hanzari zai koma kasarsa idan yana mataimakin wani a wani wajan musammanma idan jagorancin Barcelona zai yi.
Guadiola na jawabin ne gabanin Fafatawar Manchester City Da Arsenal a gumurzun mataki na hudu na Kofin FA da za su fafata a daren yau Jum’a a filin wasa na Etihad.
Kafin kama aikin sa a Arsenal a shekarar 2019, Arteta dai tsohon Mataimakin Guadiola ne a Manchester City .
A wani lamarin kuma, Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Mai 39, Sun Kama Barayin Da Suke Barnar
Shedikwatar tsaro ta ce dakarun hadin gwiwa na Operation Delta Safe, sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur 39 a yankin Kudu maso Kudu cikin makonni biyu da suka gabata.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo janaral Musa Danmadami, ya bayyana haka a wani taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis din nan a Abuja