Shedikwatar tsaro ta ce dakarun hadin gwiwa na Operation Delta Safe, sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur 39 a yankin Kudu maso Kudu cikin makonni biyu da suka gabata.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo janaral Musa Danmadami, ya bayyana haka a wani taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis din nan a Abuja.
Danmadami ya ce sojojin da ke gudanar da aikin Operation Octopus Grip da sauran ayyuka sun lalata tanda 48, tankunan ajiya 103, ramukan duga-dugan 27 da kuma kwale-kwalen katako guda 33 a lokacin.
KARANTA HAKANAN Gwamnatin Tarayya Zata Kashe Biliyan 600 Domin Gyaran Matatun Mai
Ya ce sojojin sun kuma kwato kwale-kwale guda daya, jirgin ruwa, injinan fanfo 3, jiragen ruwa masu sauri uku da motoci 13.
A cewarsa, sojojin sun kwato litar danyen mai lita 274,000, da lita 71,000 na Man Fetur, Motoci 15, AK47, yayin da aka kama mutane 40 da ake zargin masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne.
“Dukkan kayayyakin da aka kwato da wadanda ake tuhuma an mika su ga hukumar da ta dace domin ci gaba da daukar mataki,” inji shi.
“Hakazalika, rundunar sojin sama na Operation Delta Safe ta kai farmaki ta sama zuwa wasu wuraren da ake tace wa ba bisa ka’ida ba a kananan hukumomin Gogokiri Degema da Okrika duk a jihar Ribas tsakanin 12 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan.
“Crew sun lura da wuraren da suke aiki suna ganin tantuna masu motsi da kuma ayyukan tacewa ba bisa ka’ida ba.
“An kai harin ne da makamai kuma an ga wuraren sun fashe ne a wata gobara yayin da aka lalata kayan aikin tacewar da ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.
A yankin Kudu maso Gabas, kakakin rundunar sojin kasar ya ce sojoji da sauran jami’an tsaro sun ci gaba da kai farmaki kan ayyukan haramtacciyar kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra da Eastern Security Network a yankin.
Ya ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda shida, tare da kame 24 da kuma kubutar da wasu fararen hula 16 da aka sace.
A cewarsa, an kuma gano wasu nau’ikan makamai da alburusai da suka hada da bindigogi kirar AK47, bindigogi masu sarrafa kansu, bama-bamai da bututun bama-bamai na cikin gida da dai sauransu. (NAN)
A Wani Labarin Kuma 2023: Wani Dan Takarar Gwamna Ya Koma Ga Mahaliccinsa
Dan takarar gwamna a jam’iyyar NRM ta kasa reshen jihar Adamawa Alhaji Aliyu Maina ya rasu.
Olusola Afuye, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar taNRM ne ya tabbatar da mutuwar Maina.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa, na zuwa kasa da kwanaki 30 kafin babban zaben wata mai zuwa.