Kungiyar Kwallon ta Manchester United dake da matsugunni a kasar Ingila, ta cimma matsaya a kan wanda zai maye gurbin zakaran dan wasanta Paul Pogba.
Masu ruwa da tsaki a kungiyar sun yanke shawarar maye gurbin Paul Pogba da Dan wasan Kasar Croatia mai taka a Barcelona, Rakitic.
Yanzu haka dai Manchester, ta nuna kwadayin daukar dan wasan suna sauraren mai zai fito daga bakin Barcelona.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta matse kaimi wajen ganin ta dauke Pogba da Kungiyar sa ta Manchester United.
Duk da dai har yanzu babu wata nunanniyar magana a kasa akwai yiwuwar Pogba zai tsallaka zuwa Sufaniya.