Wani matashi ya koka bayan budurwarsa da yake matuƙar so ta guje shi.
Matashin wanda ya bayyana cewa yana matuƙar son budurwar tasa, yace bai yi wa budurwar tasa laifin komai ba amma ta saka masa da wannan cin amanar.
Matashin a cikin takarda da ya aikowa shafin Northern Hibiscus a manhajar Facebook, ya bayyana irin tsantsar son da yake yiwa budurwar tasa.
Yace tunda suka fara soyayya duk idan ya zo yin sallah sai yayi tunaninta, sannan yana sanyata cikin addu’ar sa, kuma bai taɓa yi mata ƙarya ba.
A cewar saurayin har abokan sa duk ya rabu da su saboda sun nuna masa ya rabu da ita, sannan ya tafka asarori sosai a dalilinta.
A kalamansa:
“Malama don Allah a gayawa matannan su ji tsoron Allah, ta karya min zuciya ba tare da wani dalili ba. Sama da wata huɗu ta bar ni ina ta son ta wallahi ɓan taɓa sallar da bana tunaninta ba tunda na fara soyayya da ita, kullum cikin yi mata addu’a nake, wallahi ɓan taɓa yiata ƙarya saboda ina mugun son ta, na rabu da abokai na saboda sun ce na kyaleta.”
“Yanzu haka na rasa abubuwa da dama saboda bani da sauran ƙwarin guiwa, wallahi ban san yadda zan gyara hakan ba. Ta bar wani ciwo wanda ba wanda zai iya warkar da shi.”
Adam Hadi Ibrahim ya rubuta:
“Addu’ar ce bata karɓuwa tunda tunaninta kake har a gurin sallah”
Hussaina Musa Garba ta rubuta:
“ALLAH ya yayema ka dage da addu’a sosai.Gaskiya ba dadi na tausaya maka”
Ummahanee Muhammad Bala ta rubuta:
“Ya Allah kada ka jarrabemu da abinda ba zamu samu ba matsalar soyayya maganinta daya ne kasamu abinda kake so din baya gashi sai dai hakuri”
Amarya Ta Fasa Auren Angonta Ana Gobe Biki Bayan Ta Gano Wani Ɓoyayyen Sirri
A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta watsawa angonta ƙasa a ido bayan ta fasa auren sa ana gobe biki, ta gano wani ɓoyayyen sirri dangane da shi.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta soke aurenta ana saura kwana ɗaya biki, bayan ta gano wani ɓoyayyen sirri dangane da angon.
Matashiyar budurwar bata san cewa bashi ya yiwa angonta katutu ba, har sai da wata budurwa ta kawo musu ziyara.