Wani dattijon Ango mai suna Alh. Muhammad Sabo ya angwance da wata yarinya shakaf, mai suna Farida.
Auren dai an ɗaura ne a jiya Juma’a 5 ga watan Mayu na shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani direban Ƙaramar mota ya gudu da jami’in kare haɗura na ƙasa wanda aka fi sani da jami’in road safety.
Hotunan bikin wannan dattijon angon da amaryar tasa ya karade kafafen sada zumunta daban daban in da da yawa mutane suka tafa albarkacin bakin su.
Da yawa na bayyana cewar tabbas an cuci yarinyar nan da aka bata wannan dattijon ta aura domin kwata kwata bazata san menene aure ba, a nasu ra’ayin.
Wasu kuma na kallon cewar dattijo ya kwashi dami a ƙala ganin cewar ya tsufa amma ya samu yarinya shakaf ya kuma wuff da ita.
Hotunan wanda za a iya cewa samfurin hotunan nan na kafin aure wato ‘pre wedding pictures’ yaja hankalin waɗan da suka bibiyi wannan hotunan.
A WANI LABARIN KUMA: Wata uwar amarya ta fashe da kuka a dai dai lokacin da za a tafi kai ‘yartata gidan mijinta.
Uwar amaryar wacce aka hango ta ta rungume’ ƴar tata a wani yanayi na bankwana da ƴar domin tafiya ibadar aure.
Hakan dai ya faru ne a wani fefen bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta na zamani.
Tun da farko dai ‘yarce tazo wajen mahaifiyar domin yiwa mahaifiyarta sallama da kuma neman a saka mata albarka a tafiyar ibadar da zata yi.
Mahaifiyar tayi kokarin riƙe kanta kar ta yi hawaye a gaban ƴartata amma hakan yaci tura.
Bayan da ta gama rungume yar ne, sai kawai aka hango ta ta ɗauki gefen mayafinta ta rufe fuskarta tana kuka.
Ita ma ƴar an hango ta tana nata kukan rabuwa da mahaifiyar tata a dai dai lokacin da ƴaruwarta ta rike hannunta domin tafiya da ita.
Ita kanta ƴar uwar amaryar an hango yanayin nata ya canza tana shirin zubar da nata hawayen.
Bidiyan ya samu makallata da dama inda wasu da yawa suka tofa albarkacin bakin su akai.