Dan wasan gaba na Nijeriya, Odion Ighalo wanda ya kammala zamansa na aron shekara guda a Manchester United ta Ingila, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al-Shabab da ke Saudiya.
Dan wasan mai shekaru 31 ya kulla kwantiragin shekara biyu da rabi da Al-Shabab daga Shanghai Shenhua ta China.
Kungiyar ta Al-Shabab ta lashe gasar zakarun Saudiya har sau shida, yayin da take sa ran samun karin taimako daga Ighalo.
Ighalo ya taka leda a kungiyoyi daban-daban irinsu Watford da Granada, yayin da burinsa na doka kwallo a Manchester United ya cika.
A wata hira da aka yi da shi a can baya, dan wasan ya ce, tun yana karamin yaro yake da burin buga kwallo a Manchester United.
A yayin bankwana da Manchester United, dan wasan ya ce, zai ci gaba da kasancewa magoyin bayan kungiyar har abada.