Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Olukayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarnin tura kwamishinonin ‘yan sanda 35 zuwa sassan jihohin kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya rabawa manema labarai a Abuja a daren ranar Talata, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Hajjin 2023: Alhazan Najeriya 813 Sun Tashi Daga Kasar Saudiyya
Sanarwar ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan amincewa da shawarar da IGP ya bayar ga hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda”.
Ya bayyana cewa, IGP din ya bada tabbacin cewa nadin ya yi daidai da jajircewar shugabancin ‘yan sanda na tabbatar da ingantaccen aikin ‘yan sanda, tsaro da kuma tabbatar da doka da oda a Najeriya.
Daga cikin sabbin kwamishinonin ‘yan sandan da aka nada sun hada da CP Adelesi E. Oluwarotimi zuwa rundunar jihar Kwara; CP Adebola Ayinde Hamzat zuwa ga rundunar ‘yan sandan jihar Oyo; CP Augustina N. Ogbodo zuwa rundunar jihar Ebonyi; CP Samuel Titus Musa zuwa Rundunar Jihar Kebbi.
Sannan akwai CP Aderemi Olufemi Adeoye zuwa rundunar jihar Anambra; CP Auwal Musa zuwa jihar Bauchi; da CP Alamatu Abiodun Mustapha zuwa Rundunar Jihar Ogun.
Sauran sun hada da CP Margaret Ochalla zuwa sashin damfara na ‘yan sanda na musamman Annex dake Lagos; CP Banji Ogunrinde ne zai jagoranci sashin hada bama-bamai; CP Rhoda A. Olofu zuwa sashin ‘yan sandan Hukumar Tashoshin Ruwa ta Yamma dake Legas; da kuma CP Kareem Musa zuwa Interpol Annex dake Legas.
An aika CP Audu Dabigi ga Rundunar sintiri a kan iyaka; CP Abibo D. Reuben zuwa Rundunar ‘Yan Sanda ta Wayar tafi da gidanka; CP Adekunle Ismaila Olusokan zuwa sashin jindadin ‘yan sanda na FHQ dake Abuja; CP Omolara Ibidun Oloruntola zuwa sashin damfara na musamman FCID Abuja.
Kazalika akwai CP Abaniwonda S. Olufemi zuwa mataimakin sakataren tsaro da sauransu.
IGP ya tuhumi kwamishinonin ‘yan sandan da aka nada da su ba da muhimmanci ga manufofinsa, hangen nesa ga rundunar ‘yan sandan Najeriya tare da ba su damar ba da fifiko ga tsaro da jin dadin ‘yan kasa da suke yi wa hidima, tare da tabbatar da bin ka’idojin adalci, kwarewa da mutunta hakkin dan Adam.
Yayin da ya bukace su da su zama shugabanni masu koyi da juna, da samar da kyakkyawar alaka da sauran hukumomin tsaro, shugabannin al’umma, da masu ruwa da tsaki.
IGP ya dora musu alhakin inganta ayyukan ‘yan sanda da ke karkashin leken asiri, da dabarun yaki da laifuffuka, da tsare-tsare na cudanya da al’umma da za su kara amincewa da jama’a da rundunar ‘yan sandan Najeriya.
A wani labarin kuma, An Yi Ram Da Wasu Mutane 8 da Ake Zargi Da Farmakar Motar Sintirin ‘Yan Sanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kame wasu mutane 8 da ake zargi da taimaka wa wani hari da aka kai kan wata motar sintiri ta ‘yan sanda.
Kai farmakin ya biyo bayan da wani mutum da ake zargi ya tsere a cikin birnin Katsina.