Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba Alkali, ya umurci kwamandojin rundunar daga bangare daban daban, da su miƙa jerin sunayen ‘yan sandan da ke aikin zabe a Anambra amma ba a biya su albashi ba.
Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da wasu jami’an ‘yan sanda suka yi kan rashin biyansu alawus-alawus na zaben gwamnan jihar Anambra.
Sama da ‘yan sanda 30,000 ne aka tura domin gudanar da zaben da ke gudana a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: BUK ta karawa wasu ma’aikatan ta 772 girma
A wata hira da aka yi da shi a Cibiyar bunkasa Dimokuradiyya a yau Asabar, Kakakin Rundunar, Frank Mba, ya ruwaito babban Sifeton na danganta rashin biyan bashin da kuskuren wasu manyan su wajen mika bayanansu.
Frank Mba ya ce sama da 29,000 na ma’aikatan da aka tsara domin gudanar da zaben sun karbi alawus-alawus din su.