Ilimi ne kaɗai makamin yaƙi da talauci da rashin aikin yi – Hukumar Zamfara
Shugaban hukumar ilimin bai daya na jihar Zamfara, ZSUBEB, Farfesa Nasiru Garba Anka ya bayyana ilimi a matsayin makamin yaki da fatara da rashin aikin yi, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su rubanya kokarinsu akan sa.
A cewarsa, hakan zai karawa gwamnatin jihar himma.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dole a maida yara su riƙa zuwa makaranta – Minista
Farfesa Anka ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin majalisar dokokin jihar kan ilimi da suka ziyarci hukumar domin gudanar da aikin sa ido a Gusau babban birnin jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi aiki kafada da kafada da kwamitin domin inganta harkar ilimi a jihar.
Shugaban na ZSUBEB ya yi kira ga iyaye da masu kula da su da su rika tura dakunan karatu a kodayaushe domin samun ilimin kasashen yamma da na Musulunci domin su zama masu amfani ga al’umma.
Da yake jawabi tun da farko, shugaban kwamitin majalisar dokokin jihar mai kula da harkokin ilimi, Hon Nasiru Abdullahi Maru ya yabawa gwamnan jihar Dauda Lawal bisa hangen nesa da ya yi na nada wanda ya cancanta kuma gogaggen wanda zai yi aiki a matsayin shugaban UBE na jihar.
A cewar shugaban kwamatin, wannan ne karon farko da aka nada farfesa da zai jagoranci al’amuran hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa, ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa Anka zai kai matsayin ilimi zuwa mataki na gaba.
A wani labarin kuma:Za’a samu buji na kwanaki 3 daga ranar Alhamis – NiMet
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun buji daga ranar Alhamis zuwa Asabar a fadin kasar.
Yanayin NiMet da aka fitar ranar Laraba a Abuja ya yi hasashen buji a yankin arewa ranar Alhamis a duk lokacin hasashen.