Hukumar Ba da Lamuni ta Duniya (IMF) ta amince da bayar da dala miliyan 447.39 ga Kenya bayan nazarin shirinta na ba da lamuni ga kasar , kamar yadda asusun ya bayyana a ranar Talata. Kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da bashin Kenya ya fara raguwa saboda ci gaban da aka samu a kasafin kudi.
KARANTA WANNANBLABARIN: Dan Takarar Gwamnan Arewa Ya Gana Da Yan Jiharsa Mazauna Abuja
Amma a cikin wata sanarwa da asusun ya fitar ya bayyana cewa ya ware karin wasu kudade a karkashin wani shiri na musamman ga Kasar ta Kenya.
Yayin da kasar dake yankin Afirka ta Gabas ta kulla yarjejeniyar samar da kudade na tsawon watanni 38 tare da asusun ba da Lamuni na Duniya a watan Afrilun bara, kudaden da aka fitar na baya bayan nan ya kai dalar amurka biliyan 1.65, yanzu dai Kenya za ta samu jimillar dala biliyan 2.416 daga yarjejeniyar da aka kulla.
Kana Gwamnatin Shugaba William Ruto, wacce ta karbi ragamar mulki a watan Satumba, na shirin rage rancen kasuwanci masu tsada domin samun albarkatu masu rahusa kamar bankin duniya don rage matsi na biyan basussukan kudaden shiga.
Rahotanni sun nuna cewa tattalin arzikin Kenya ya kasance mai cikin wani yanayi, kuma ana sa ran zai karu da kashi 5.3 a cikin wannan shekara.
Sai dai kuma agefe guda asusun ba da lamuni na Majalissar dinkin duniyan, ya kara da cewa ana sa ran hauhawar farashin kayayyaki ya karu a kasar Kenya nan da farkon shekarar 2023.
A wani labari kuma, Ku Taimakawa Ƙokarin Samar Da Jami’o’i Masu Zaman Kan Su – Sarkin Kano
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, yayi Kira ga mawadata su tallafawa kokarin gina Jami’o’i masu Zaman kansu da wasu mawadata keyi a jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan Kiran ne a wajan taron Kaddamar da littafin tarihin rayuwar Shugaban rukunin kamfanonin AZMAN Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina wanda aka yiwa lakabi da (RESILIENCE) aka kuma gudanar da taron a dakin taro na Jami’ar Bayero dake Kano.
Mai martaba Sarkin yace gina irin wadannan jami’oi a masu Zaman kansu a jihar Kano zai taimakawa dalibai su samu guraben karatu bayan kammala makarantun sakandire.
A don hakane ma ya yabawa Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina bisa samar da wannan jami’a, Yana mai cewa hakan zai cigaba da habaka ilimi a jihar Kano, tare da godewa wadanda suke akan gaba wajan gina irin wadannan jami’oi masu Zaman kansu