Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana fatan ganin an gudanar da babban zaben na bana cikin kwanciyar hankali, da kuma barinsa karagar mulki, tun da ya gamsu da tsarin mulkin kasar na wa’adi biyu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Shugaban ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin jakada na musamman na shugaban kasar Evariste Ndayishimiye na kasar Burundi wanda ya zo da sako a cikin mako guda.
Buhari ya ce Najeriya za ta tallafa wa Burundi ta hanyoyi daban-daban kamar yadda ya kamata, yana mai cewa hakan zai kasance cikin ruhin hadin kai da ‘yan uwantaka a Afirka.
KU KARANTA KUMA Buhari Ya Jajantawa Wadanda Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Ritsa Da Su
Ministan Kudi, Kasafin da tsare tsaren tattalin arziki na Burundi, Mista Audace Niyonzima, ya ce shugabansa ya aika sakon fatan alheri ga ‘yan Najeriya da kuma shugaba Buhari.
Ya kuma yi wa kasar fatan alheri a babban zaben da aka shirya yi a watan Fabrairu da Maris na wannan shekara.
“Muna addu’ar Allah ya sa zaben ya kasance cikin kwanciyar hankali da nasara, ta yadda Najeriya za ta ci gaba da rike sunanta a matsayin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji jakadan na musamman.
Dangane da bukatar taimako a fannin samar da makamashi musamman man fetur da shugaban kasar Burundi ya gabatar, shugaba Buhari ya ce ya san yadda kasar ke fama da karancin makamashi.
Don haka ya yi alkawarin cewa zai sa kamfanin man fetur na Najeriya Ltd. ya duba wannan bukata.
A ranar Talata ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 21.83 da kuma karin lokacin amfani da kasafin kudi na shekarar 2022.
Kamfanin Dillancin labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa kasafin kudin 2023 shine na karshe da gwamnati mai ci ta shirya yayin da take zuwa karshe.
Yayin da yake rattaba hannu a kan kasafin, shugaban ya ce an kara yawan kudaden da aka kashe na Naira Tiriliyan 21.83 da Naira Tiriliyan 1.32 bisa shawarar farko na kashe Naira Tiriliyan 20.51 da bangaren zartarwa ya yi.
A Wani Labarin Kuma Makomar Kiristoci Na Cikin Hatsari A Zaben 2023 – Fasto
Babban mai kula da Cibiyar Bishara ta Duniya ta Dunamis, Fasto Paul Enenche ya ce zaben 2023 ya wuce na zahiri ya koma zuwa na tsafi.
Fasto Eneche da yake magana a yayin taron hadakar cocin sa na watan Janairun 2023, a Glory Dome da ke Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, ya bayyana cewa makomar Kiristoci na cikin hadari a zaben 2023.