Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana gamsuwarsu a kan shawarar da gwamnatin tarayya ta dauka na rufe iyakokinta da makwabtan kasashe, tare da bayyana hakan a matsayin hanya daya tilo da Nijeriya za ta tilasta yin biyayya ga dokokinta na yaki da shigo da kayayyaki ba bisa ka’ida ba.
Sarki Sanusi ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai a fadarsa domin jinjina wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan nada sabbin membobin kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (EAC).
Sarki Sanusi ya zargi kin biyan gwamnati haraji da wasu ‘yan kasuwa masu shigo da kaya ke yi da rashin isassun matakan tsaro a iyakokin Nijeriya, sannan ya kara da cewa rashin tsaro a iyakokin ya bawa barayin albarkatun man fetur saukin fita da kaya daga Nijeriya.
“Ina goyon bayan yin hakan dari bisa dari. Rufewar ta wucin gadi ce, kuma za ta kawo wa kasa ci gaba.” A cewar sarki Sanusi.
Da yake magana a kan sabbin membobin EAC, Sarki Sanusi ya ce shugaba Buhari ya yi abin da ya dace ta hanyar nada kwararrun masana tattalin arziki, da suka san ciki da wajen tattalin arzikin Nijeriya, a cikin sabon kwamitin. A cewarsa, shugaba Buhari ya dauki matakin da ya dace ta hanyar zabo kwararrun masana tattalin arziki masu basira domin bashi shawarwari a kan gyaran tattalin arzikin kasa a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar barazana saboda adawar kasuwanci a tsakanin wasu manyan kasashe.
Sarki Sanusi ya bayyana membobin kwamitin a matsayin masu gogewa a bangaren tattalin arziki, tare da bayyana cewa yana da yakinin cewa zasu farfado da tattalin arzikin Nijeriya.