Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ne mi a fuwar yan Najeriya kan kalaman da yayi kan yan kabilar Fulani. Kamar yadda Punch ta ruwaito
Ortom ya ne mi gafarar ne a yau Laraba jim kadan bayan tawagar Gwamnonin 5 na Jam’iyar PDP dake adawa da dan takarar Jam’iyan na shugaban kasa, sun ziyarci Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun Kama Wanda Yayi Yunkurin Kai wa Ayarin Atiku Hari a Maiduguri— Yan sanda
Wannan dai na zuwa ne Biyo bayan sukar da suka biyo bayan kalaman gwamnan na jihar Benue, inda ya bayyana cewa ba zai goyi bayan wani dan kabilar Fulani ba a matsayin dan takarar shugaban kasa. yayin da yake magana kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a kwanakin Baya.
Ortom wanda yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a Bauchi, a wani taron tuntuba da kungiyar ‘G-5 Integrity Group’ ta yi, ya ce: “Ina so in ce maganar da mutane ke yi ba ita ce abin da nake nufi ba a lokacin da na yi wadannan kalaman .
“Amma duk daya, na san cewa zai kai ga rashin fahimta. Ina so in ce wa wadanda suka ji haushin maganganuna, su yi hakuri. Ba haka nake nufi ba,” inji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Birtaniya Ta Biya Diyyar Kashe Kananan Yara 64 A Afghanistan
Gwammanatin Birtaniya ta biya diyyar mutuwar mutane da suka rasa rayukansu A Afghanistan wanda ya zarce yawan yaran da suka rasa rayukansu a ƙasar da kusan sau huɗu.
Gwamnatin kasar ta bayar da diyyar ne ta mutuwar yara 64 , adadin da ya zarce mutum 16 ɗin da ta bayyana ta amince da su.