Akalla mutane 174 ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a wasan kwallon kafa a Indonesia tsakanin Arema FC da Persebaya Surabaya, bayan da ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa fusatattun magoya bayan kungiyoyin kwallom daga filin wasan. Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a Malang, inda magoya bayan kungiyar Arema, suka mamaye filin wasa bayan da kungiyar ta sha kashi na farko a gida a hannun Persebaya Surabaya cikin shekaru 23.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Zan Kara Biyan Duk Wani Malamin Dake Yajin Aikin ASUU Ko Si-Sin Kwabo Ba—Gwamna Tambuwal Ya Fusata
Da yake mayar da martani ga farmakin kakkin rundunar Yan sandan kasar ya ce, ‘yan sandan sun harba barkonon tsohuwa a filin wasa da kuma tasoshin filin wasan wanda ya haifar da firgici a tsakanin jama’ar inda suka fara tserewa daga hanyoyin gita filin wasan.
Ana shi bangaren Shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo, a wani shirin talabijin na Al Jazeera wanda wakilin Majiyar Dimokuradiyya ya sanyawa ido, ya dakatar da dukkan wasannin La Liga 1 na kasar har sai an kammala bincike.
Idan dai ba a manta ba, hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta hana sanya hayaki mai sa hawaye a filayen wasan kwallon kafa.
Kazalika Rahotanni sun bayyana cewa, wasu mutane sun shake, wasu kuma aka tattake su yayin da daruruwan suka ruga neman hanyar fita da nufin tserewa daga cikin sinadarin da yan sandan suka harba, daga cikinsu akwai kananan yara da da dama..
Da yake mayar da martani game da wannan mummunan lamari, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniha wato FIFA Gianni Infantino, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rana a tarihin kwallon kafa.
A WANI LABARI KUMA: An Samu Ɗaure-Ɗauren Aure Sama Da 1,500 A Cikin Watanni 8 A Abuja – AMAC
Hukumar rajistar aure ta karamar hukumar Abuja (AMAC) ta ce an yi wa aure 1,522 rajista a hukumance tsakanin watan Janairu zuwa Agusta a yankin.
Mista Akinwumi Akintayo, babban magatakardar aure na AMAC ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.