Cibiyar yada labarai ta kasa da kasa (IPC), ta sake yin kira da a gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kaiwa wata kafar yada labarai wacce ake kira da Thunder Blowers da Mansur Rabiu, wanda ke aiki a matsayin editan yada labarai a gidan Jaridar dake garin Gusau, Babban Birnin jihar Zamfara.
An zargi mutane takwas da hannu a harin da aka kai a farkon watan nan a garin Gusau, na jihar Zamfara.
Harin da aka ce, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito, ya kai ga jikkata editan gidan Jaridar, wanda ya tsira da ransa.
Hakan ya sa Babban Darakta na IPC, Lanre Arogundade, a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai ciki har da Jaridar DAILY POST a ranar Talata, ya ce lamarin ya kasance “abin takaici”, yana mai cewa harin da ake kaiwa ‘yan jarida ba zai zama “abun da za’a kyale bane, duk da mun shiga sabuwar shekara ”
Ya jaddada cewa “ya kamata a nemo wadanda ke da hannu a wannan harin kuma a hukunta su”.
Ya bukaci “a gudanar da cikakken bincike kan wannan harin da wasu hare-haren da ba a san ko suwaye ba suka kai ba kan ‘yan jarida.”
Baya ga kiran da ya yi na a gudanar da cikakken bincike, ya ce a biya ‘yan jaridar da abin ya shafa diyya tare da sauya wa gidajen Jaridar kayan aikinsu da suka lalace.