IPOB tace Ƴan Ta’adda sun kai harin Gidan Yarin Kuje ne domin su hallaka ƴaƴan ta
Ƙungiyar Tsagerun Kafa Ƙasar Biafra IPOB a ranar Alhamis tayi martani akan shigar da ƴan ta’adda suka yi a gidan yarin Kuje dake Abuja.
IPOB tayi zargin cewa Maharan sun kai harin ne domin su kashe mambobin su da ake tsare dasu a gidan yarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Katsina: Ayarin Jami’an Tsaron Buhari basu wani yaƙi ƴan bindiga a lokacin Ƙwanton Ɓauna
Ƴan bindigar wanda akayi amannar ƴan Boko Haram ne, sun shiga gidan yarin Kuje a ranar Talata ɗauke da bam.
Ƴan Ta’addan sun saki dukkanin mambobin su dake wurin.
Da yake jawabi akan harin, Mai Magana da Yawun IPOB Emma Powerful, ta gargaɗi cewa kada wani abu ya faru da mambobin ta.
Powerful tayi gargaɗin cewa IPOB ba zata yi sauki ba, idan Gwamnatin Nijeriya ta yi wani abu daya faru da mambobin ta a gidan yarin.