Iyaye da malamai sun caccaki matakin gwamnatin jihar Kaduna na yin sauya zuwa makaranta na kwanaki 4 a duk Mako, a makarantun gwamnati a fadin jihar.
A cewar iyaye da malaman da aka zanta da su, sabuwar manufar za ta yi illa ga ayyukan da daliban.
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar ilimi, Halima Lawal ta fitar, ta ce za a gyara Jadawalin karatu ta 2021/2022 domin tabbatar da daukar nauyin manhajar karatun.
Ta ce: “Duk makarantun gwamnati za su yi ƙaura zuwa na kwanaki 4 a mako, Mai makon kwanaki biyar da aka Saba da shi, yayin da za a daidaita kalandar ilimi ta 2021/2022 don tabbatar da ɗaukar tsarin karatun,” in ji ta.
Da yake mayar da martani kan wannan tsokaci, wani Uba a Rigasa da ‘ya’yansa ke zuwa makarantar gwamnati, Aliyu Suleiman, ya ce manufar za ta yi wa ‘ya’yansa illa.
“A matsayinmu na iyaye, ba mu gamsu da wannan manufar ba domin hakan zai shafi ayyukan yaranmu a makaranta.
“Ku tuba abin da ya faru a cikin 2020 lokacin da aka rufe makarantun gwamnati saboda barkewar cutar Corona, kuma yanzu yaran suna kokawa don murmurewa, gwamnati ta zo da wannan aiki na kwanaki 4,” in ji shi.
Wani Uba Mai suna Suwidi Zakari, ya ce babu shakka bambancin rana zai shafi rayuwar yaro a makarantar gwamnati.
“Wata rana na iya shafar yaron da ke zuwa makarantar gwamnati. Muna fatan gwamnati za ta sake tunani sai dai idan ba su damu da ‘ya’yanmu ba,” inji shi.
Wani malami, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya caccaki tsarin zuwa Makarantu na kwanaki 4, yana mai cewa a maimakon haka ya kamata gwamnati ta rika biyan malaman albashin su na yau da kullum ko kuma karin lokacin aikinsu na ranar Juma’a.
“Idan gwamnati na son taimaka wa malamai, za a iya yin hakan ta hanyar biyan mu karin albashin mu na yau da kullum maimakon a rage mana rana domin rana za ta yi illa ga Karatun daliban,” inji shi.
Sauran malaman da aka yi magana da su kuma suma sun yi adawa da manufar Karatu na kwanaki 4 a Mako.