Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ba da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a faɗin Ƙananan Hukumomi 13 na jihar, a matsayin wani mataki na kare rayukan dalibanta.
Hakan ya biyo bayan barazanar tsaro da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan, musamman a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda tuni Gwamnati ta mallaki rahotannin da ke nuni da cewa akwai yuwuwar barazanar tsaro a cikin al’ummar jihar da ke makwabtaka da babban birnin tarayya Abuja, kamar Gitata da Umaisha.
KARANTA WANNAN LABARIN: NAPTIP ta kama wata mata da laifin sanya Matashiya Sana’ar Karuwanci
Rufe makarantun na daga cikin Ƙudurin da aka cimma a yayin wani taron majalisar zartarwa na jihar, wanda ya gudana a gidan Gwamnati dake Lafia a ranar Laraba.
Da take yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar, kwamishiniyar ilimi ta jihar, Fatu Jimita Sabo, ta ce bayan duba halin da ƙasar nan ke ciki, musamman game da matsalar tsaro a Babban Birnin Tarayya, Gwamnatin Jihar ta yanke shawarar rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da ɓata lokaci ba.
A cewar ta, hakan ya zama wajibi idan aka yi la’akari da kusancin jihar da Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma kudurin gwamnati na ganin cewa makarantun Nasarawa, suna gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai kyau.
Sai dai ta bayyana cewa waɗanda ke azuzuwan fita, wadanda tuni suka fara rubuta jarabawar karshe, musamman a makarantun sakandare, an cire su.
Ta ce, “Muna kira ga iyaye da kada su firgita. Dukkanmu mun san jihar Nasarawa tana lafiya amma an ɗauki wannan matakin ne a matsayin wani mataki na tabbatar da ƴaƴanmu sun tsira kuma a ci gaba da zaman lafiya. Wato wadanda ke cikin jihar da waɗanda suka zo daga wasu jihohi su yi karatu a nan.
“Muna kuma kira ga shuwagabanninmu da shugabannin makarantunmu, da su kuma tabbatar da cewa yayin da muke rufe wadannan makarantu, mun yi su cikin tsari.
“Babu wata barazana ga rayuwa ko dukiya a halin yanzu a Jihar Nasarawa. Kuma kamar yadda na ambata, wani bangare ne kawai na matakan aiwatar da gwamnati. Muna sane da cewa tgwamnatin Abdullahi Sule ta ba da fifiko ga tsaro da kare rayuka da Dukiyoyin a Jihar Nasarawa.