Jakadiyar Ukraine a Amurka Oksana Markarova, ta kira Rasha a matsayin kasar ‘yan ta’adda saboda mamayewar da ta yi a Ukraine.
Ta fadi haka ne a wata hira da Jaridar Fox News a ranar Lahadi.
Ta kuma bukaci Amurka da ta taimakawa Ukraine da makamai da sauran abubuwan taimako.
“Wannan kasa ce ta ta’addanci kuma ya kamata mu dauki Rasha a matsayin ‘yan ta’adda,” in ji Markarova, a cewar Sky News.
A wani labarin Kuma na daban.
Mai horar da Tawagar Flamingoes Bankole Olowookere ya tabbatar da cewa kungiyar zata samu nasara a wasan da zata buga da ta Congo a yammacin.
Yan wasan na Nahiyar kan kasa da shekaru 17 ta mata, zata kara da kasar Congo a wasa zagaye na farko na wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya, a wasan da za’a buga a filin wasa na Stade des Martyrs.
Kocin a tattaunawa da manema labarai bayan atisayen da suka gudanar, yace ba zasu baiwa al’ummar kasa kunya ba, sabili da irin rawa da Kwazan da yan wasan ke nunawa.
Yace zamu baiwa al’ummar kasa nasaran da zata sasu farin ciki, da samun nasarar da zata kaimu Ya wasa na gaba, ina mai tabbatar da cewa yadda muke Congo zamuyi abun da za’ayi Alfahari.
Kazalika, Kyaftin din kungiyar Alvine Dah-Zossu, tabbatarwa da jama’an kasa irin shirin da sukayi gabannin wasan da Congo.
Tace a shirye suke da wasan, zamu bada dukkannin gudunmuwa tare da yin alkawarin yin nasara ga kasa.
Muna bukatar goyan bayan ku kuma bazamu bada kunya ba, a cewar rahoton.