Hukumar shirya jarabawar shiga mayan makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta sanar da dage ci gaba da rajistar DE, wadda ta shirya rufewa ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu, 2023, amma ta kara da mako guda,Vanguard ta rawaito.
Hukumar ta ce yanzu haka za a ci gaba da atisayen a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, 2023,sakamakon lokacin yin jarabawar gama gari ta UTME 2023 da kuma aikin kidayar jama’a na kasa zai kare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bamu Da Bukatar Kwankwaso a APC – Dan Bilki Kwamanda
“Wannan ci gaban an yi shi ne domin a dauki nauyin gudanar da jarabawar UTME, wadda aka sanya wa hannu za a fara ranar Talata 25 ga watan Afrilu, 2023, kuma za ta kare ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, yayin da ake shirin fara kidayar jama’a a ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, kuma za’a kammala ranar Juma’a, 5 ga watan Mayu, 2023,”
Hukumar ta bayyana hakanne a cikin wata sanarwa,a ranar Lahadi, ta hannun mai magana da yawunta, Fabian Benjamin.
Sanarwar ta ce: “Saboda haka, an umurci ‘yan takarar da ke son yin rajista don aikin DE don tabbatar da cewa sun sami DE ePINs daga wuraren sayar da kayayyaki da aka keɓe a ko kafin 30 ga watan Afrilu, 2023, lokacin da za a rufe sayar da ePIN. Ana sa ran ‘yan takarar za su wuce ofishin hukumar daga ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, 2023, zuwa ranar Asabar, 13 ga watan Mayu, 2023, don kammala aikin rajistar su.”
“Hukumar ta tabbatar wa duk masu son yin rajistar DE cewa babu wanda za a hana shi damar yin rajista matukar ya bi umarnin hukumar da kuma cikin wa’adin da aka kayyade.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hakazalika, hukumar ta nemi fahimtar ‘yan takara yayin da ta samar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin duba yadda ake samun gurbatar sakamako, bayanai da sauran laifuka,” in ji sanarwar.
A wani labarin kuma, Matawalle Ya Mayar Da Sarkin Yodoto, Bayan Dakatar Da Shi Tsawon Watanni
Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da Alhaji Aliyu Garba Marafa a matsayin Sarkin Birnin Yandoto.
A watan Yulin shekarar da ta gabata, Matawalle ya dakatar da sarkin saboda ya ba wani sarkin ‘yan fashi, Ado Aleiru mukamin sarauta.